Turkiyya ta gamsu da sulhun da Itopiya da Eritiriya suka yi

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwa inda ta ce, ta gamsu da yadda Itopiya da Eritiriya suka yi sulhu da juna.

Turkiyya ta gamsu da sulhun da Itopiya da Eritiriya suka yi

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da sanarwa inda ta ce, ta gamsu da yadda Itopiya da Eritiriya suka yi sulhu da juna.

Sanarwar ta ce "Tun shekarar 1998 Itopiya da Eritiriya suka yanke mua'amala amma a yanzu sun yin sulhi tare da sasanta juna bisa kokarin Shugaban Kasar Eritiriya Isaias Afwerki da Firaministan Itopiya Abiy Ahmed. Turkiyya ta gamsu matuka da yarjejeniyar da aka sanya hannu a kai a birnin Jedda na Saudiyya a ranar 16 ga Satumban 2018."

Tun bayan da Eritiriya ta samu 'yancin kai daga Itopiya a 1993 kasashen 2 suka fara rikicin kan iyaka inda a shekarun 1998-2000 suka yanke huldar jakadanci. 

A shekarar 2000 sun sanya hannu a Aljeriya amma aka gaza aiki da ita.Labarai masu alaka