Iran ta aike wa Isra'ila wani sako mai razanarawa

Babban kwamanda na biyu na dakarun sojinIran Huseyin Salami ya bayyana cewar har abada gwamnatin yahudawan Isra'ila ba za ta taba yin nasara.

Iran ta aike wa Isra'ila wani sako mai razanarawa

Babban kwamanda na biyu na dakarun sojinIran Huseyin Salami ya bayyana cewar har abada gwamnatin yahudawan Isra'ila ba za ta taba yin nasara.

A sanarwar da Salami ya bayar da kamfanin dillancin labarai na Fars ya sanar da irin bayanan da ya yi ga masu shiga soji na sa kai inda ya ce, Isra'ila ba za ta wa Iran barazana. Hizbullah kadai sun isa su shafe su daga ban kasa. Ya kuma zargi gwamnatin tel Aviv da yaudarar duniya game da Iran.

Salami ya kara da cewar Amurka ta ware dala tiriliyan 7 don yaki a gabas ta Tsakiya amma kuma an cinye su duk da haka kuma a duk inda babu sansaninsu to Iran ce ta ke da karfi a wajen.

Salami ya kuma ce, yana kira ga Firaministan gwamnatin Uahudawa da ya gwada ninkaya a tekun Mediterrenean saboda har abada Isra'ila ba za ta taba yin nasara ba.

A jawabin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya fara gangamin adawa da Iran. Kuma za su shiga Siriya, Iraki da ma ko'ina don magance Iran.

Netanyahu ya kuma nuna wasu hotuna inda ya ke ikirarin Iran na ci gaba da sarrafa sinadaran Nukiliya a kasarta.

Amma Ministan Harkokin Wajen Iran Jawab Zarif ya mayar da martani kan ikirarin na Netanyahu inda ya ce, wani wasan kwaikwayo kawai ya yi a wajen kuma kamata ya yi Isra'ila ta mayar da hankli kanta game da batun Nukiliyar.

 Labarai masu alaka