Al'ummar Faransa sun ƙalubalanci salon mulkin Macron

An gudanar da zanga-zangar ƙalubalantar salon mulkin shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a fiye da garuruwa 100 a fadin ƙasar.

Al'ummar Faransa sun ƙalubalanci salon mulkin Macron

An gudanar da zanga-zangar ƙalubalantar salon mulkin shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a fiye da garuruwa 100 a fadin ƙasar.

Zanga-zangar da kungiya mafi girma a kasar ta tarayyar ma'aikata (CGT), da kuma Solidaires da Force ouvrieres suka kira ya samu halartar dinbin al'ummar kasar domin ƙalubalantar kudurorin da salon mulkin Macron.

Dubun dubatan mutane da suka haɗa da maaikata, yan makaranta, yan kasuwa da masu karbar fensho sun halarci wannan zanga-zangar da aka gudanar a fiye da gurare 100 a kasar.

Kafar yaɗa labaran Montparnasse da na ƙasar ltaliya ta bayyana cewar daga cikin masu tarzomar sun dinga jifar yan sanda da duwatsu a babban birnin kasar Paris.

Ƴan sandar sun mayar da martani ta hanyar amfani da barkonon tsohuwa inda suka bayyana kame mutane huɗu da kuma raunanan mutane biyu.

Kamar yadda ƴan sanda suka sanar kungiyoyi dubu 11 da 500 da kuma mutane dubu 50 suka halarci zanga-zangar.

Dalibai 20 daga jami'ar Sorbonne dake Paris sun rufe kofar shiga jami'ar dake Tolbiac tun da misalin karfe 7.30 har zuwa ƙarfe 10.00. Haka kuma a jami'o'in dake garuruwan Rennes, Lyon da Montpellier an gudanar da makamantan haka.

A yayinda sakataren CGT Philippe Martinez ke kalubalantar yunkurin sauye-sauyen gwamnatin kasar ya bayyana cewar lokaci ya yi da mata zasu fara karbar albashi daidai da maza amma Macron bai san da haka ba.


A yan kwanakin da suka gabata an dinga zuwa yajin aiki domin kalubalantar sabbin tsarukan gwamnatin Faransa musamman a watan Mayu da Yuni inda miliyoyin al'ummar kasar suka tafi yajin aiki tare da gudanar da zanga-zanga.Labarai masu alaka