Amurka da Katar sun buɗe sabuwar shafin hurɗa da juna

A ganawar da ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi da ministan tsaron kasar Katar Halid Bin Muhammed el-Atiyye a Washington an taɓo hurɗar ƙasashen biyu da kuma lamurkan yankin baki ɗaya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauert ta bayyana cewar ministan tsaron Katar ya gana da Pompeo da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.

A yayinda minista Pompeo ke ganawa da ministan tsaro da mataimakin firaministan Katar an tattauna akan lamurkan tsaro da samar da lumana a yankin baki daya.

A ganawar an nuna irin muhimmanci dake ga kungiyar haɗin gwiwar ƙasashen gulf domin samar da lumana a gabas ta tsakiya.

Bugu da ƙari, a ganawar Pompeo da Atiyye an tattauna akan yadda ƙasashen biyu zasu yi aiki bai ɗaya domin bunkasa harkokin tsaron samaniya ta El-Udeyd da kuma yadda ƙasashen biyu zasu rinka muhimman aiyuka bai ɗaya.

Ministan tsaron Katar ya kuma gana da takwaransa na Amurka James Mattis.

Tag: hurda , Katar , Amurka

Labarai masu alaka