Rashin lafiyar Shugaban Kasa ta janyo an yi wa Kundin Tsarin Mulkin Gabon kwaskwarima

Sakamakon tafiyar Saudiyya don duba lafiyarsa da Shugaban Kasar gabon Ali Bongo ya yi, an fara yunkurin ba wa mataimakinsa damar jagoranci wanda hakan ya sanya aka yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar.

Sakamakon bukatar da Firaminita Emmanuel Issoze Ngondet ya mika, kotun kundin starin mulki ta bayar da damar wasu aiyukan Bongo ga mataimakinsa Pierre-Claver Maganga Moussavou.

Shugabar kotun Kundin Tsarin Mulki  Marie Madeleine Mborantsua ta yanke hukuncin da ya ba wa mataimakin Shugaban Kasar damar yi wasu aiyuykan mai gidansa dake kwance a asibiti a Saudiyya.

A karkashin hukuncin kotun, idan Shugaban Kasa ba ya nan to Shugaban majalisar Dattawa zai jagoranci Kasar na kwanaki 30 zuwa 60 kuma a wannan lokacin dole a gudanar da sabon zabe.Labarai masu alaka