An rantsar da Maduro a matsayin shugaban ƙasar Venezuela

An rantsar da Nicolas Maduro wanda ya lashe zaben shugaban ƙasar Venezuela da aka gudanar a ranar 20 ga watan Mayu.

An rantsar da Maduro a matsayin shugaban ƙasar Venezuela

 

An rantsar da Nicolas Maduro wanda ya lashe zaben shugaban ƙasar Venezuela da aka gudanar a ranar 20 ga watan Mayu.

An rantsar da shi ne a babban kotun ƙasar dake Caracas babban birnin kasar.

A rantsar da Maduro Wanda ya lashe zaben da kaso 68 a turmin farko wanda kuma zai ja ragamar mulkin ƙasar har shekarar 2025 ya samu halartar mataimakin shugaban ƙasar Turkiyya Fuat Oktay.

 

Haka kuma bukin ya samu halartar shugaban kasar Bolivia Juan Evo Morales, na Cuba Miguel Mario Diaz-Canel da kuma wakilai daga misalin ƙasashe 90.

 

Daga cikin waɗanda sunka kaɗa kuri'a miliyan takwas Maduro ya samu miliyan shida.

Sauran yan takarar kuwa da sunka haɗa da Henry Falcon ya samu kuri'a miliyan 1 da dubu 820, Javier Bertucci ya samu dubu 925, Reinaldo Quijada kuwa ya samu kuri'a dubu 34 da 614.

 

Gwamnatin Nicolas Maduro zata fuskanci ƙalubalen tattalin arziki da kuma na siyasa, buga da ƙari zata yi fama da matsalolin diflomasiyya a yankin da kuma saka hannayen jari.

 

 Labarai masu alaka