"Iran ba zata taba zama boyar Amurka ba"

Ministann harkokin wajen Iran Muhammed Jevad Zarif ya bayyana cewar Iran ba zata taba kasancewar yadda Amurka ke so ba, ya kuma kamata Amurka ta amince da Iran ba kawarta ba ce.

Jewad Zarif ya bayar da amsa akan kalaman da ministan harkokin wajen Amurka ya yi akan Iran. Inda yake cewa:

"A duk inda Amurka ta sanya kafarta babu abinda ke faruwa sai rikici da tashin hankula" wannan kalaman na Zarif amsace ga kalaman Mike Pompeo da yake neman Iran ta sauya zuwa "kyakkyawar" kasa.

"Iran ba zata taba amincewa da kaidojin Amurka ba, ba zata taba zama kasa tamkar yadda Amurka da Mike Pompeo ke bukata ba. Saboda haka ya kamata Amurka ta amince da ta rasa Iran a fagen hurda"

A yayinda ministan harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fita rangadi a gabas ta tsakiya ya fara yada zango a jordan inda ya bayyana cewar suna bukatar Iran ta koma "kyakyawar" kasa

Pompeo ya kara da cewa, "Za mu ninka matsin lamba a kan Iran ba kawai a fannin diflomasiyya kawai ba, har ma a fannin kasuwanci."

Tag: siyasa , Iran , Amurka

Labarai masu alaka