Rasha na kokonton ko Amurka zata janye sojojinta daga Siriya

Rasha ta bayyana cewar duk da Amurka ta nuna kamar zata janye sojojinta daga Siriya amma ga dukkan alamu tana neman wani uzuri da zai sanya ta ci gaba da zama a ƙasar.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Rasha Mariya Zaharova a yayin da take sharhi akan harkokin yau da kullum ta bayyana cewar.

Shugaban ƙasar Amurka ya bayyana cewar zai janye sojojin ƙasarsa daga Siriya a watan jiya, amma kasancewar rashin sanin ainihin alkiblar ta Amurka babu tabbas din zata janye sojojin nata daga Siriya.

Zaharova, a halin yanzu Amurka tana yin kamar zata janye sojojinta daga Siriya amma kuma tana nan tana neman uzurin da zai sa ta ci gaba da zama a ƙasar.

Zaharova ta ƙara da cewa tabbas janye sojojin Amurka daga Siriya mataki ne daya dace.

 Labarai masu alaka