Amir Khan ya kawo ziyara Turkiyya

Mashahurin tauraron fim na masana’antar fina-finai ta kasar India Bollywood, milyoniya Amir Khan ya kawo ziyara birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Amir Khan ya kawo ziyara Turkiyya

Mashahurin tauraron fim na masana’antar fina-finai ta kasar India Bollywood, milyoniya Amir Khan ya kawo ziyara birnin Istanbul na kasar Turkiyya.

Jarumin wanda ya yi bulaguronsa a cikin wani jirgin kamfanin Turkish Airlines  ta kasar Turkiyya, ya bayyana cewa yana matukar murnar ziyartar Turkawa.

Amir Khan ya ce zai gana da taurarun fina-finan kasar Turkiyya, kana ya nuna sabon fim dinsa.

A lokacin da ya sauka a filin tashi da saukar jiragen sama na Atatürk da ke Santambul,Khan ya gaisa da dubban masoya wadanda suka yi cuncurundo domin yin masa oyoyo,inda ya sa musu hannu tare daukar hotuna da ma’abotansa.

 Labarai masu alaka