Najeriya ce kasar da za ta fi kowacce kasa a duniya yawan matalauta a 2018

Wani hasashe da kungiyar "World Poverty Clock" ta yi ya nuna cewa, nan da shekarar 2018 Najeriya za ta zama kasar da ta fi kowacce kasa a duniya yawan mataalauta.

Najeriya ce kasar da za ta fi kowacce kasa a duniya yawan matalauta a 2018

Wani hasashe da kungiyar "World Poverty Clock" ta yi ya nuna cewa, nan da shekarar 2018 Najeriya za ta zama kasar da ta fi kowacce kasa a duniya yawan matalauta.

Rahoton da Kungiyar ta fitar ta ce, nan da watan Fadrairun 2018 Najeriya za ta zama tana da yawan mutanen da ke cikin talauci da suka kai miliyan 83 wanda a yanzu suka kai miliyan 82.

Hakan na nuna cewa, yawan matalutan Najeriya a shekarar 2018 zai haura na Indiya wanda zai kama miliyan 82.3.

Shafin yanar gizon kungiyar na worldpoverty.io ya bayyana cewa, sun yi amfani da alkaluman hukumomşnkasa da kasa wajen tabbatar da wannan batu tare da fitar da sakamakonsa.

A yanzu dai naajeriya na da yawan mutane miliyan 193, kuma yawan al'umar kasar na dadu wa da kaso 2.63.Labarai masu alaka