An sayar da Lu'u-Lu'u mallakar Saliyo kan dalar Amurka miliyan 6.5

An sayar da Lu'u-Lu'u mallakar kasar Saliyo kan kudi har dalar Amurka miliyan 6.5. Lu'u-Lu'un na daya daga cikin mafiya girma a duniya da aka gyara su.

Shugabar Kamfanin Sarrafa Jauhari na Ingila Graff Diamonds mai suna Laurence Graff ce ta sayi Lu'u-Lu'un wanda gwamnatin Saliyo ta ce tana son ta gudanar da aiyukan more rayuwa da kudinsa.

Za a yi amfani da rabin kudin wajen samar da ruwan sha mai tsafta, lantarki, makarantu da asibiti a kauyen Koryardu da ake ciro Lu'u-Lu'u wanda ke yankin gabashin Saliyo.

An yi gwanjon kadarar a birnin New York na Amurka.Labarai masu alaka