Swizalan za ta dawo wa da Najeriya dala miliyan 321 da aka kwace daga wajen iyalan Abacha

Gwamnatin Swizalan ta bayyana cewa, za ta mayar wa da Najeriya dalar Amurka miliyan 321 wanda na daga cikin dukiyoyin da aka kwace daga hannun iyalan tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya marigayi Janaral Sani Abacha.

Gwamnatin ta Swizalan ta sanar da hakan ne a ranar Litinin din nan inda ta ce, an dauki matakin bayan wata yarjejeniya da aka yi da Babban Bankin Duniya.

Kungiyar Yaki da Cin Hanci ta Tranparency International ta zargi marigayi Sani Abacha da satar kudade har dalar Amurka biliyan 5 a lokacin da ya ke kan mulki.

A shekarar 2014 gwamnatin Najeriya tare da iyalin Abacha suka amince kan za a dawo wa da Najeriya kudadenta wadanda aka tsare su a banki bayan tuhumar dan tsohon shugaban Abba Abacha da ake yi a kotu.

Kotun Swizalan ta tuhumi Abba Abacha da laifin satar kudaden, damfara da saba dokoki ta'ammuli da kudade a shekarar 2005 bayan an dawo da shi daga Jamus inda ya kwashe kwanaki 561 a kasar.

A shekarar 2006 kotun ta Swizalan ta bayar da umarnin daskarar da kudaden na Abba Abacha.

A yanzu dai za a dawo wa da Najeriya wadannan kudade.Labarai masu alaka