Yara kanana da ke dauke da cutar Kanjamau a Afirka ba sa samun kulawar da ta kamata

A wani rahoto da Asusun tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar an bayyana cewa, kowanne 4 daga cikin yara kanana 5 da ke dauke da cutar Kanjamau a Yammaci da Tsakiyar Afirka ba ya samun maganin "antiretroviral".

Asusun ya yi gargadi da cewa, wannan magani shi ne ke hana masu dauke da cutar Kanjamau mutuwa, inda kuma kasashen Yammaci da Tsakiyar Afirka ke baya wajen kula da lafiyar masu dauke da wannan cuta ta HIV/AIDS musamman ma ga yara kanana.

Rahoton ya ce, a shekarar 2016 akwai akalla yara kanana dubu 60,000 da cutar ta kama a yankunan.

Asusun ya ce, mutane da ke da shekaru 15 zuwa 19da ke dauke da cutar Kanjamau sun fi 'yan shekaru 0 zuwa 14 yawa. 

Rahoton ya kara da cewa, yankunan Yammaci da Gabashin Afirka ne ke dauke da kaso 25 cikin 100 na yara masu shekaru 0-14 da ke dauke da cutar Kanjamau a duniya.Labarai masu alaka