Turkiyya da Somaliya sun amince da habaka Tattalin Arzikinsu

Gwamnatocin Turkiyya da Somaliya sun sanya hannu kan yarjejeniyar habaka Tattalin Arzikinsu.

Turkiyya da Somaliya sun amince da habaka Tattalin Arzikinsu

Gwamnatocin Turkiyya da Somaliya sun sanya hannu kan yarjejeniyar habaka Tattalin Arzikinsu.

Mataimakin Firaministan Turkiyya Recep Akdag tare da takwaransa na Somaliya Mahdi Muhammad Gulaid ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

A jawabin da ya yi, Akdag ya ce, Turkiyya ta zuba jari a Somaliya na sama da dalar Amurka miliyan 100 inda ya ce, a wannan shekarar suna sa ran ya kai dala miliyan 200.

A nasa jawabin Gulaid ya ce, taron zai kara habaka alakar kasashen 2 a shekaru masu zuwa.

A ranar Juma'ar nan ne aka fara babban taron kasuwanci na Turkiyya-Somaliya a birnin Ankara karkashin jagorancin Akdag da Gulaid.Labarai masu alaka