Wata Tunkiya ta haifi 'ya'ya biyar Rigiz a Turkiyya

Wata Tunkiya a yankin gundumar Kavaklidere ta lardin Mugla na Turkiyya ta haifi 'yan biyar wanda hakan ya ba wa al'uma matukar mamaki.

Wata Tunkiya ta haifi 'ya'ya biyar Rigiz a Turkiyya

Wata Tunkiya a yankin gundumar Kavaklidere ta lardin Mugla na Turkiyya ta haifi 'yan biyar wanda hakan ya ba wa al'uma matukar mamaki.

Mai Tunkiyar Kasim Yilmaz ya sanar da mai dakinsa Sengul Yilmaz kan abun mamakin bayan da ya ga Tunkiyar na haihuwar 'ya'ya daya bayan daya.

Kasim Yilmaz ya bayyana cewa, sun dade suna kiwon dabbobi kuma wannan ne karo na 2 da Tunkiyarsa ta ke haifar 'yan biyar inda a baya ma sun taba samun haka.

Makiyayan dai a cikin farin ciki inda jama'a masu sha'awar kallo suke zuwa ganin Tunkiyar da 'ya'yanta biyar rigiz.Labarai masu alaka