An gina layin dogon jirgin kasa da ya ke bi ta cikin gini mai hawa 19 a China

A garin Chongchinag na Kasar China an gina hanyar jirgin kasa da ta bi ta cikin wani gini mai hawa 19 wanda ya ke jan hankalin jama'ar duniya.

Aikin ginin layin dogon da ya ratsa ta hawa na 3 na ginin na daukar mutane a kowacce rana.

An dauki matakin yadda karar jirgin ba za ta damu jama'a da suke zaune a ginin ba.

An bayyana cewa, jirgin kasan na amfani da tayoyin mota ne mai maikaton karafa da jiragen kasa suka saba amfani da su.

Wannan abu dai na jan hankali jama'ar China da ma 'yan yawon bude ido da ke zuwa Kasar.

Tag: Ajabi , Mamaki , China

Labarai masu alaka