Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jamme a kasuwa

Gwamnatin Gambiya ta sanar da yin gwanjon mota da jirgin sama mallakar tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh.

Gambiya ta sanya motoci da jirgin saman tsohon Shugaban Kasar Jamme a kasuwa

Gwamnatin Gambiya ta sanar da yin gwanjon mota da jirgin sama mallakar tsohon Shugaban Kasar Yahya Jammeh.

A yanzu mota da jirgin na kasuwa ga duk masu son saya.

Ministan Kudi na Gambiya ya bayyana cewa, an sanya motocin dasuka hada da samfurin Hummer Rolls Joyce a kasuwa.

Ministan ya kara da cewa, baya ga motocin akwai jirgin sama na karami na musamman mallakar Jammeh wanda shi ma an sanya shi a kasuwa ga duk mai bukata.

An bayyana cewa, an yi wa motocin lamba da sunan Jammeh, matarsa da ‘ya’yansa.

Jammeh dai ya mallaki manyan motoci masu numfashi sama da 10.

Asusun Bayar da Lamuni na Duniya IMF dai ya bayyana cewa, tattalin arzikin Gambiya ya fara farfadowa amma kuma ana bin kasar basuka da yawa.

 Labarai masu alaka