Amurka ta sanar da sabbin takunkuman murkushe Iran

Bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da fitarsu daga yarjejeniyar Nukiliya da Iran, Ma'aikatar Baitulmalin Kasar ta sanar da sabbin takunkuman tattalin arziki ga Iran.

Ma'aikatar ta sanar da cewa, an saka sunayen wasu mutane 6 da kamfanunnuka 3 da suke da alaka da gwamnatin masu tsaurin ra'ayi ta Iran a jerin sunayen da ke kan bakar takarda.

Matakin da Amurkan ta dauka wajen takunkumin ya hada da: Meghdad Amini, Muhammed Hasan Hodai, Said Najafpur, Mesud Nikbaht, Fuad Salihi da Muhammadrıza Hedmati Valadzaghard.

An bayyana cewa, wadannan mutane suna da alaka kai tsaye da Iran da kuma Dakarun Kudus.

Janaral Kassim Sulayman dan kasar Iran da ke jagorantar Dakarun Kudus tun 2007 ya shiga na jerin sunayen mutanen da Amurka ta dauka a matsayin 'yan ta'adda.

Ma'aikatar Baitulmalin ta kuma sanar da cewa, Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gano yadda Iran ta aika da miliyoyin daloli ga Dakarun Kudus. 

Kafin a sanar da sabbin takunkuman Shugaban Kasar Iran Hassan Ruhani ya bayani da cewa, saka musu sabbin takunkumai ya saba wa sashe na 2231 na dokokin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya da dokokin kasa da kasa.

 Labarai masu alaka