Turkiyya na sarrafa da fitarda ingantaccen magani zuwa kasashen waje

Fannin fitar da magani daga ƙasar Turkiyya zuwa ƙasashen ketare ya bunƙasa a yayinda a cikin shekaru biyar aka yi nasarar bunƙasa fitar da magani da kaso 16.1 cikin ɗari a inda aka yi nasarar cinikin dala miliyan 875.3.

A ƴan shekarun da suka gabata sashen magani ya samu bunƙasa a fannin saka hannun jari a ƙasar.

Kayan magani da suka haɗa da vitamin, antibiotic, jini, ruwan jiki, allurai, kayan ƙarin ruwa da makamantansu anyi nasarar fara fitar dasu zuwa nahiyoyi biyar

A cikin shekaru biyar Turkiyya ta fitar da magani har na dala biliyan 4.1.

A cikin shekaru biyar Turkiyya tayi nasarar samun ƙaruwar fitar da kayayyakin magani da kaso 16.1 cikin ɗari da karuwar ciniki na dalla miliyan 875.3, kasar da tafi sayarwa da magani itace Koriya ta Kudu da cinikin dala miliyan 136.4 sai Iraq da cinikin dala miliyan 64.6, Swiss da dala miliyan 55.3 sai kuma Jamhoriyar Demokradiyyar Cyprus da dala miliyan 30.5.

 Labarai masu alaka