Farashin man fetur na ci gaba da tashin gauron zabi

Farashin gangar danyen man fetur na ci gaba da hauhawa a kasuwannin duniya, yayin da Amurka ke fama da karancin makamashi,wanda ba a taba ganin irin sa ba tun a watan Satumbar shekarar 2016.

Alkalumman Hukumar makashi ta EAI sun nuna cewa a ranar Larabar nan da ta gabata,Amurka na gurbin gangunan mai milyan 12,6 da ya kamata ta cika.

Tsadar man fetur dai ta samo asali ne daga kungiyar kasashen masu arzikin man fetur OPEP wacce ta rage yawan makamashin da ya kamata ta sayar a shekarar 2019 da kuma rashin masu saye.

 Labarai masu alaka