An kama jirgin ruwan China na kama kifaye ba bisa ka'ida ba a gabar tekun Saliyo

An kama wani jirgin ruwan China na kama kifayen a gabar tekun Saliyo da ke yammacin Afirka ba bisa ka'ida ba.

An kama jirgin ruwan China na kama kifaye ba bisa ka'ida ba a gabar tekun Saliyo

An kama wani jirgin ruwan China na kama kifayen a gabar tekun Saliyo da ke yammacin Afirka ba bisa ka'ida ba.

Kwamandan sojin ruwan Saliyo, Sallieu Kanu ya bayyana cewa, an kama jirgin tun daren Alhamis din da ta gabata.

Ya ce, masu kama kifi na kasar ne suka fara bin bayan jirgin wanda masuntan cikinsa suke lalata ragar kamun kifinsu.

'Yan kasar ta China sun ba wa 'yan Saliyo cin hanci amma suka ki karba inda nan da nan suka kira sojin ruwan Saliyo wadanda suka zo suka kama masuntan na China da ke kamun kifaye ba bisa ka'ida ba.

Ya ce, ba wannan ne karo na farko da ake kama 'yan kasar waje na kama kifaye a tekun Saliyo ba bisa ka'ida ba.

A watan Afrilun 2017 an kama wasu jiragen ruwa 4 na 'yan kasar waje a gabar tekun.Harkokin kama kifi a Saliyo na samar da aiyuka ga mutane sama dubu 36, kamar yadda Bankin Duniya ya sanar.

A kowacce shekara Saliyo na asarar dala miliyan 50 sakamakon kama kifaye a tekunta ba bisa ka'İda ba da ake yi.Labarai masu alaka