"Ba dan mu ba da Gabas ta Tsakiya ta shiga-uku"

Donald Trump, ya yi wa kasashe masu arzikin man fetur barazana da su gaggauta kawo rahusa a farashin wannan makamashin,wanda a yanzu haka, yake ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya,ko kuma Amurka ta daina zama gatarsu.

"Ba dan mu ba da Gabas ta Tsakiya ta shiga-uku"

Shugaba kasar Amurka,Donald Trump, ya yi wa kasashe masu arzikin man fetur barazana da su gaggauta kawo rahusa a farashin wannan makamashin,wanda a yanzu haka, yake ci gaba da tashin gwauron zabi a kasuwannin duniya,ko kuma Amurka ta daina zama gatarsu.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter,shugaban na Amurka, ya nuna kasashen Gabas ta Tsakiya da ma Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur OPEC da yatsa,inda ya ce:

"Ba dan mu ba da kasashen Gabas ta Tsakiya sun shiga-uku.Saboda mu ke tabbatar da tsaronsu.Amma sai ga shi suna ci gaba da zage damtse wajen kara farashin man fetur a ko yaushe.Dole ne mu tunatar da su.Tilas ne OPEC ta gaggauta sauke farashin man fetur".,

Wannan ba shi karo na farko ba da Trump ya zargi OPEC da zama silar mahaukaciyar hauhawar farashin man fetur.Labarai masu alaka