An bayyana waɗanda suka fi kowa arziki a China

An bayyana Jack Ma shugaban kanfanin Alibaba a matsayin wanda ya fi kowa dukiya a kasar China.

An bayyana waɗanda suka fi kowa arziki a China

An bayyana Jack Ma shugaban kanfanin Alibaba a matsayin wanda ya fi kowa dukiya a kasar China.

Binciken da kamfanin Harin dake Shangay ta gudanar ta bayyana Ma wanda ya mallaki yen biliyan 270 a matsayin ja gaban masu arziki a kasar.

Wanda aka bayyana mafi arziki a bara Shu Chian mai kamfanin gidaje wato Guangcou ya zo na biyu a bana da mallakar yen biliyan 250 wato dala biliyan 36.

 Mai kamfanin kimiyya da fasaha wato Wechat Tencent mai suna Pony Ma ya zo na uku da mallakar yen biliyan 240 wato dala biliyan 35.

A ɗayan barayin kuma, a yayinda daga cikin mutane goma da suka fi arzikin aka samu mutane biyu sun yi kunnen doki ya sanya an fitar da mutane 11.

Dukiyar mutane goman a jumlace ya kama dala biliyan 255.

Daga cikin su kashi 28.7 cikin ɗari mata ne wacce aka bayyana a matsayar macen da tafi ko wacce arziki a kasar a Bara Yang Huiyen ta kasance mace mafi dukiya a bana da mallakar dala biliyan 22.Labarai masu alaka