Nijar ta ba wa wani kamfanin China damar neman Yuraniyom a kasar

Gwamnatin Nijar ta ba wa wani kamfani hakar ma'adananai na China lasisin neman albarkatun man Yuraniyom a yankin Tchirozerine dale arewacin kasar.

Nijar ta ba wa wani kamfanin China damar neman Yuraniyom a kasar

Gwamnatin Nijar ta ba wa wani kamfanin hakar ma'adananai na China lasisin neman albarkatun man Yuraniyom a yankin Tchirozerine dale arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Nijar (ANP) ya bayyana cewa, sakamakon hukuncin da aka dauka a Majalisar Ministoci an ba wa kamfanin Zijing Heuchuang na China lasisin neman albarkatun man Yuraniyom a yankin filayen Toulak da Terzemour.

Kamfanin na China zai zuba jarin Yuro miliyan 4.5 a yankin na Tchirozerine mai arzikin man Yuraniyom.

China na kan gaba wajen neman albarkarun kasa da suka hada da man fetur a Jamhuriyar Nijar.Labarai masu alaka