Kisan Kashoggi: Amurka ta kakaɓawa 'ƴan ƙasar Saudiyya 17 takunkumi

Amurka ta ɗauki matakin kakaɓawa ƴan ƙasar Saudiyya 17 takunkumi akan kisan ɗan jarida Jamal Kashoggi

Kisan Kashoggi: Amurka ta kakaɓawa 'ƴan ƙasar Saudiyya 17 takunkumi

Amurka ta ɗauki matakin kakaɓawa ƴan ƙasar Saudiyya 17 takunkumi akan kisan ɗan jarida Jamal Kashoggi

Ma'aikatar harkokin kuɗin ƙasar Amurka ta bayyana cewar wadanda suka taka rawa game da kashe Jamal Kashoggi an miƙa sunayensu a jerin sunayen wadanda suka take hakkokin bil'adama.

Fadar gwamnatin Amurka ta bayyana cewar daga cikin waɗanda ta kakkaɓawa takunkumi sun haɗa da tsohon mai bada shawara ga yarima mai jiran gado Muhammed Bin Salman wato Suud el -Khatani, jakadan Saudiyya a ofishin jakadancin Saudiyya dake lstanbul Muhammed el -Khatibi da mataimakinsa Mahir Mutreb  a jeren sunayen kuma da Salah Tubaigy, Meshal el-Bostani, Naif el-Arifi, Mohammed el-Zahrani, Mansour Abahussain, Khalid el-Otaibi, Abdulaziz el-Hawsawi, Waleed el-Sehri, Thaar el-Harbi, Fahad el-Balawi, Badr el-Otaibi, Mustafa el-Madani, Saif el-Qahtani da Turki el-Sehri.

Takunkumin ya kunshi kwace dukiyoyinsu dake Amurka da kuma haramta su gudanar da kasuwanci da dukkanin kamfanonin kasar.

Ya kamata mu lura da takunkumin ya zo ne bayan kwanaki 45 da kashe Jamal Khashoggi.

 Labarai masu alaka