Malaman makaranta sun gudanar da zanga-zanga a Girka

Malaman makaranta sun gudanar da zanaga-zanga a Atina babban birnin kasar Girka domin kalubalantar yunkurin canja musu yanayin aiki, da yawansu dai sun kwash artabu da 'yan sanda.

Tare da kira ga kungiyoyi daban daban malaman makaranta sun gudanar da tanzoma inda sunka yi cincirindo a tsakiyar birnin kasar da yankin Sintagma. Dubun dubatan malaman na kalubalantar dokar da zata canja musu yanayin aiki.

Da farko dai sunyi kira ga firaministan kasar Alexis Tsipras da kuma ministan ilimin kasar Kostas Gavroglu daga bisani kuma sunka yi tattaki har izuwa majalisar kasar da kuma titin da ofishin firaministan yake.

Masu zanga-zanagar da sunka yi arangama da 'yan sanda, inda sunka so su kutsa da motocinsu a titunan da 'yan sandar sunka rufe lamarin daya sanya karo jami'an tsaro da sunka yi amfani da barkonon tsohuwa.

A lokacin wannan tarzomar mutane biyu sun sami raunuka kamar yadda kafafen yada labaran kasar sunka rawaito.

 Labarai masu alaka