Turkiyya ta bai wa marayun Albaniya 2000 tallafin kudi

A ranar Asabar din nan da ta gabata,kungiyar bada agji ta kasar Turkiyya,IHH ta bai wa marayun kasar Albaniya 2000 tallafin kudi.

Turkiyya ta bai wa marayun Albaniya 2000 tallafin kudi

A ranar Asabar din nan da ta gabata,kungiyar bada agji ta kasar Turkiyya,IHH ta bai wa marayun kasar Albaniya 2000 tallafin kudi.

IHH ta raba taimakon tare da tallafin kungiyar kasar Albaniya "Alternative Foundation of the Future" (ALSAR), mataimakin shugaban IHH reshen Albaniya, da kuma mataimakin jakadan Turkiyya da ke Tirana,babban birnin kasar,Gul Sarigul .

A yayin da yake jawabi,Sarigul ya ce huldar da ke tsakanin Turkiyya da Albaniya da na karfi sosai,da fatan za ta dauwama a haka don bukatar al'umomin kasashensu 2.

Shi kuma shugaban ALSAR cewa yayi, yana kyautata zaton marayu da dama za su amfana da irin wannan tallafin a 'yan shekaru masu zuwa.

 ALSAR wacce aka kafa shekarar 2006,ta fara aiki a shekarar 2008,inda tunda daga wannan lokaci ya zuwa yanzu suka share kwallan marayu 3,141.Labarai masu alaka