Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Kakakin shugaban kasar Turkiyya Ibrahim Kalın ya fitar da sa sanarwa ta shafinsa na Twitter inda ya ce, sakamakon wannan mummunan lamari Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Turkiyya kizilay da kuma Kungiyar Turkish Red Crescent sun tafidon bayar da taimako.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, a ziyarar da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan zai kai kasar Rasha za a tatttauna batutuwan da suka shafi kasashen biyu da ma na kasa da kasa. Kakakin shugaba Erdoğan Ibrahim Kalin ya ce,a tsakanin ranakun 13 da 15 ga Nuwamba ne Erdoğan zai ziyarci Rasha inda zai gana da takwaransa na kasar Vladimir Putin.Ya ce, da fari shugaba Erdoğan zai gana da Putin a Sochi. A yayin ganawar za a tattauna batutuwan cinikayya da kasuwanci da ke tsakanin kasashen, batun makamashi da na janye wa juna visar shiga kasashen. Bayan ziyarar Rasha shugaban na Turkiyya zai wuce zuwa Kuwait.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yildirim a yayin ziyarar da ya kai Amurka ya amsa tambayoyin dan jaridar CNN Fareed Zakariyya. Mai gabatar da shirin ya yi tambaya game da yadda Amurka ta ce ba ta ga laifin shugaban 'yan ta'addar FETO ba kuma ba shi da hannu a yunkurin juyin mulkin Turkiyya, sai Yildirim ya bayar da amsa da cewa, Turkiyya ta bayar da amsa da irin halayar da aka nuna bayan hari 11 ga Satumba. Ya ce, turkiyya ce kasa ta farko da ta nuna za ta bayar da taimako, amma babu wanda ya tambayi sai an bayar da shaida kan cewa Alqa'eda kuniyar ta'adda ce.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, mataimakin firaministan Turkiyya mai kula da cigaban tattalin aerziki Mehmet Şimşek ya bayyana cewa, Turkiyya za ta sam makudan kudade daga kasashen waje,wanda hakan zai sanya kasar ta karfafa wa masu zuba jarin kasashen waje. Ya tunatar da cewa, a 2014 Hukumar baitulmalin Turkiyya ta samar da tsari mai kyau wanda za a fora a kansa don cigaban tattalin arzikin kasar.Labarai masu alaka