Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan tare da takwaransa na Rasha Vladimiri Putinsun gana a birnn Sochi nda suka tattauna kan batun kasar Siriya. Shugabanin 2 sun aike da sakonnin neman mafita. Bayan ganawar shugaba Erdoğan ya ce, sun samu damar tattauna batutuwa da suka shafi rarrabuwar kai a Siriya. SUn amince da hada kai wajen warware rikicin ta hanyar siyasa. Putin kuma ya ce, da shi da Erdoğan suna da tunani iri daya na ganin an warware rikicin ta hanyar siyasa.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yildirim ya tattauna ta wayar tarho mataimakin shugaban kasar Iran mai matsaya na daya Ishak Jihangir inda ya mika sakon ta'aziyya da jajen wadanda suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta afku a iyakar Iraki da Iran. Majiyoyin fadar firaministan sun ce, Yildirim ya shaidawa Jihangir yadda Turkiyya ta damu game da wannan lamari, kuma za su ci gaba da kasance wa tare da Iran a koyaushe. Ya ce, Turkiyya a shirye ta ke da ta bayar da taimako.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Kamfanin Bayar da Shawarwari da Bincikar Harkokin Haraji na PriceWaterhouseCoopers (PWC) ya fitar da wani rahoto game da wadanne kasashe ne za su zama a sawun gaba wajen cigaban tattalin arziki a shekarar 2050. Idan aka dubi karfin saye da sayarwa to a shekarar 2050 Turkiyya za ta zama kasata 10. Turkiyya ta bar kasashen Turai da dama a baya sakamakon irin kokarin da ta nuna. Duk da irin halin da aka shiga a 2017, ammakasar za ta habaka sosa musamman a shekarar 2015.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, za a mayar da jirgin ruwa samfurin Kartal II wanda a shi ne Mustafa Kamal Ataturk ya fara bayar da isharar yakin kwatar 'yancin kai, inda ya ce, jitragen kasashen yamma masu kutse da suka shiga gabar tekun Istanbul za su koma inda suka fito kamar yadda suka zo.

 Labarai masu alaka