Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a jawabin da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi a wajen taronranar nakasassu ta duniya ya bayyana cewa, ba shi da wata matsala game da takaita zirga-zirgar kudade. Amma babbar matsalar shi ne ta 'yan ta'addar FETO da na PKK da ke fataucin kudade daga Turkiya zuwa kasashen waje. Ya ce, abin ya bayyana wa jama'a shi ne 'yan kasuwarsu su tsaya tsayin daka wajen ganin sun nuna kishin kasa. Erdoğan ya kara da cewa, kofar Turkiyya ta kasuwanci a bude ta ke a kowanne bangare.Tun daga shekarar 1989 ake da 'yancin fitar da kudade daga Turkiyya zuwa kasashen waje kuma ana ci gaba da hakan.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Shugaban Kungiyar Masu fitar da kayayyaki ta yankin tekun Black Sea Ahmet Hamdi ya bayyana cewa, a watanni 11 na wannan shekarar sun fitar da kayayyaki zuwa kasashen duniya 112. A wata rubutacciyar sanarwa da ya fitar shugaban ya ce, an dibi kayayyaki daga yankunan Trabzon, Rize, Artvin da Gümüşhane a tsakanin watan Janairu da Nuwamban bana. Kuma yawan darajarsu ta kai ta dalar Amurka biliyan 1 da miliyan 297 da dubu dari 797.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, dan wasan ninkaya ta marasa hannu dan kasar Turkiyya Beytullah Eroğlu ya sake samun nasara a wasan ninkaya na duniya da aka gudanar wanda shi ne na farko a duniya da ya yi nasarar lashe wannan gasa. Sanarwar da hukumar Shirya Wasannin Paralmpik na Nakasassu ta Duniya ta fitar ta ce, a yayin gasar da aka shirya a Mekziko dan kasar ta Turkiyya ya yi ninkayar ya y nasara kan abokan hamayyarsa a ninkayar mita 50. A gasar mita 100 kuma beytullah Eroğlu ya zo na 4.

 Labarai masu alaka