"Sai dai a kashe tsohuwa kan daddawarta"

Shugaba kasar Turkiyya Recep ya nuna bacin ransa game da wutar fitinar da Trump ya hura a Kudus,inda ya tunatar da takwaransa na Amurka cewa bai da hurumin mallaka wa Yahudawa wannan tsarkakken birnin.

Shugaban na Turkiyya wanda ya yi magana a gaban dubban 'yan kasarsa ya yi jawabi kamar haka :

"Ya kai Trump,me kake tsammanin cewa ka aikata, da ka yanke shawarar mallaka wa Yahudawa birnin Kudus ? Idan tunaninka, ka mallaki gaskiya tunda kana da karfi,to ka sani cewa ka yi matukar nisa a cikin duhun jahilci.Domin baka da hurumin yin hakan.Ai duk daniya ta san da cewa, mai gaskiya ne ke da karfi,ba bai karfi ke da gaskiya ba.Na gana da shugabannin Turai da na Duniyar Islama, har ma da Papa Roma Francis don tattaunan wannan batun.Kudus ita ce al-kiblar farko ta duniyar Islama.Sai dai a kashe tsohuwa kan daddawarta,domin ba zamu taba kasa a gwiwa ba a wajen kwato hakkinmu.Don a wanan karon, mun fi kowa gaskiya"Labarai masu alaka