Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep tayyip Erdoğan ya gana da ma'aikatan kamfanin jiragen saman Turkish Airlines da ke kasashen waje a fadarsa ta Beştepe. A jawabin da ya yi, Erdoğan ya ce, idan kamfanunnuka na son su yi fice a duniya to dole ne su zama masu daga kasashen da suka fito. Ya ce, Turkish Aililes da ke zuwa kowacce kusurwa ta duniya ya samu nasarar shiga ran al'Umarsa. Kuma ya samu irin wannan nasara a duniya baki daya. 

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Bayan sojojin Rasha da na Siriya sun kai hari a Idlib, Turkiyya ta gayyacai jakadun Siriya da Rasha da ke Ankara don jin ba'asi. Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta gayyaci jakadan Rasha Aleksey Yerhov da na Siriya Muhammad Ibrahim. Ma'aikatar ta mika takardar korafi ga Rasha da Siriya game da karya dokar yarjejeniyar Astana da kasashen Iran, Rasha da Turkiyya suka amince da ita na Idlib ya zama yankin da ba za a dinga rikici a cikinsa ba. Turkiyya ta nuna wa jakadun matukar bacin ranta kan wannan abu.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Ministan tsaro na Turkiyya Nurettin Canikli ya ce, dakarunsu suna da garkuwar tsaro daga makamai masu linzami, amma kumagarkuwar S-400 na da kyau da inganci sosai. Ya bayar da amsa ame da cin bashin sayen garkuwar S-400 da cewa, ai an same su a farashi mai inganci.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Tsohon Garin Pamukkale Mai tarihi da ke jerin sunayen wuraren tarihi na Hukumar Raya Al'adu ta Majalisar Dinkin DUniya UNESSCO na ci gaba da tarbar maziyartansa masu yawon bude ido da tsari mai kyau. A yanzu Pamukkale na da kyawawan wajen wanka na zamani a koramun da ke wajen. Kuma ruwan wajen ko da sanyi ko da zafi na zama a yanayin zafin digiri 36 a ma'aunin Ceicius.Labarai masu alaka