Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya mayar da martani ga majalisar shura ta harkokin shari'a ta Amurka kan kin mika wa Turkiyya shugaban 'yan ta'addar Fethullah FETO/PDY. Wadannan mutane da suka ba wa kansu hukunci na siyasa su ne suke tashi su soki Turkiyya. Erdoğan dai ba zai taba girmama hukuncinku ba, kuma ba zai yarda da shi ba saboda babu adalci a ciki.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yidirim ya bayyana cewa, za a kara yawan manyan kotuna guda 9 na kasar zuwa 15. A jawabin da ya yi a wajen taron majalisar shura kan harkokin shari'a ya ce, manufar hakan shi ne saketabbatar da tsaro da kuma hanzarta shari'un da ake yi. Ya ce, akwai bukatar yin wadannan abubuwa na sauye-sauye. Kuma bayan kammala tsare-tsare za su mika wa majalisa.

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya ce, ya kamata Rasha da Iran su cika alkawarin da suka yi game da kasar Siriya na goyon bayan tsagaita wuta a Idl,b. Ya ce, bai kamata a gayyaci 'yan ta'adda zuwa taron Sochi ba. Kuma Turkiyya ta ce, ba za ta je duık wani waje da aka gayyaci 'yan ta'addar PYD/YPG reshen PKK ba. Idan har aka gayyaci 'yan ta'adda zuwa Sochi to tattaunawar za ta rushe.

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, sabuwar dokar hana zaluntar dabbobi da aka samar ta tanadi cewa, duk wanda ya aikata zalunci ko kashe dabbar da ta ke da ma, ita ko mara sahibinta za a yanke masa hukuncin daurin shekaru 4.5 a gidan kaso, za kuma a iya daure wasu mutane har shekaru 7 gwargwadon abin da suka aikata na kashe dabbobin ko zaluntar su.Labarai masu alaka