Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Haber Turk na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi jawabi a wajen taron ganawa da masu unguwanni karo na 43. Shugaban ya ce, wadanda suke son kafa kasa a arewacin Siriya na cikin tsaka mai wuya. Kar wanda ya mata da yadda muka dauki wannan abu. Saboda haka duk wani da ya ce zai kafa kasa a wannan yankin to zai dibi kashinsa a hannu. 

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Çavuşoğlu ya ce, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan na son gana wa da shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel bayan an kafa sabuwar gwamnati a Jamus din. Ministan ya amsa tambayoyin 'yan jaridar Jamus a birnin Antalya inda ya ce, Erdoğan zai gayyaci Merkel ko kuma shi ya je kasar ta Jamus don gana wa da ita.

Babban labarin jaridar Star na cewa, Firaministan BulgeriyaBoyko Borisov wanda ke shugabancin Tarayyar Turai ayanzu ya bayyana cewa, akwai bukatar Tarayyar ta gyara al'amuranta da Turkiyya. Ya ce, akwai bukatar su yi aiki sosai don gyara wannan matsala da ke tsakaninsu da Turkiyya. Ya kara da cewa, Turkiyya na daya daga cikin mambobin NATO kuma ta taka rawa sosai wajen magance kwararar 'yan gudun hijira zuwa Turai.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, An kammala kaso 88 cikin 100 na aikin hanyar Gebze-Orhangazi-Izmir wanda za ta bayar da dama ga tafiya zuwa Istanbul daga Izmir ya dawo awa 3.5 mai makon awanni 9. An kammala hanyoyin karkashin kasa 17 inda ake ci gaba da aikin ba kakkautawa.

 Labarai masu alaka