"Ku zo mu kafa sabbin ginshikan samar da zaman lafiya a duniya"

Shugaba Erdoğan ya kira takwarorinsa na duniya da su zama tsintsiya madaurinki daya wajen kafa sabbin ginshikan samar da zaman lafiya a duniya.

"Ku zo mu kafa sabbin ginshikan samar da zaman lafiya a duniya"

Shugaba Erdoğan ya kira takwarorinsa na duniya da su zama tsintsiya madaurinki daya wajen kafa sabbin ginshikan samar da zaman lafiya a duniya

Shugaban na Turkiyya ya furta wannan kalamin a babban taro kan harkokin kasuwanci na duniya wanda aka shirya a birnin Santambul.

Erdoğan wanda ya yi tunatarwa kan asarar rayukan farar hula a Sham ya ce,

"Ku zo mu kafa sabbin ginshikan samar da zaman lafiya a duniya",inda daga bisani ya kira kasashen da bama-bamansu masu guba ,suka hadassa mutawar mutane da dama.

Shugaban na Turkiyya ya kira kasashen da suka haifar da asarar rayukan fararen hula da dama kana suka fi kowa ambaton zaman lafiya, da su gyara halayyansu.

Erdoğan ya tabo batun farmakan da aka wai gwamnatin Bashar Al Asad (wacce ta yi amfani da makamai mai guba) a ranar Jumma'a da safe a karkashin jagoranci Amurka inda ya ce,

"Akwai abu daya da suka sa gaba,mun kai masa farmaki ne don ya yi amfani da makami mai guba.Ka ware mutanen da aka kashe ta hanyar amfani da makaman yau da kullum gefe daya,sannan ka dinka farautar wadanda suka kashe mutane ta hanyar amfani makamai masu guba.To ina gaskiya take a nan ?"

Erdoğan wanda ya ce Turkiyya ta kashe zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan 31 wajen daukar nauyin mansu neman mafaka ya ce,Tarayyar Turai ta yi alkawarin bai wa Turkiyya dalar Amurka biliyan 6 don taya ta daukar nauyin 'yan gudun hijira, amma ba ta cika alkawarinta ba.

Daga karshe shugaban na Turkiyya ya ce,

"Kama daga azzalumai ya zuwa wadanda suka dilmeye a teku,ba mu ware kowa ,mun ji kan kowanne daga cikin su, mun bude musu kofar kasarmu.Ba mu taba kasa a gwiwa ba wajen jin tausayi kamar yadda muka saba.Mun far wa 'yan ta'addar da suka haddasa cincirindon masu neman mafaka kasarmu da kuma zama tushen duk wani aikin ta'addanci, ba tare da wata shakka ba".

 Labarai masu alaka