Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya

Babban labarin jaridar Yeni Şafak na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya bayar da sakon da ke nuna sun yanke hukunci yaki da 'yan ta'addar Fethullah FETO. A jawabin da Shugaban ya yi kafin fara babban taron jam'iyyarsa na Maltepe karo na 6 ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sun kamo mambobin kungiyar 80 daga kasashen waje. Ya ce "Kai ma shugabansu da ka ke Pensylvania za ka zo. Ka yi yawonka yadda ka ke so." 

Babban labarin jaridar Sabah na cewa, Firaministan Turkiyya Binali Yildirim a yayin taron jam'iyyar AKP na gundumar Tuzla ya yi bayani kan harin da Amurka ta jagoranta wajen kai wa gwamnatin Siriya inda ya ce, "farar daya kasashen yamma sun tuna da Siriyawa da ake zalunta. Wannan makararriyar amsa ce da aka ba wa masu kashe mutane."

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Mataimakin Firaministan Turkiyya Mai kula da harkokin cigaban tattalin arziki Mehmet Şimşek ya bayana cewa, an samu tsaro a bangaren saye da sayar da gwala-gwalai. Ya ce, a zango na 2 na tattara bayanai mutane dubu 7,100sun sayi kilogram 335 na gwal. 

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, Sakataren Kawancen NATO Jens Stoltenberg ya zanta da kamfanin dillancin labarai na Anadolu inda ya ce, Turkiyya kasa ce ma, matukar muhimmanci ga NATO. Stoltenberg ya ja hankali da cewa, suna da burin taimaka wa Turkiyya. Ya kuma yi kira ga dukkan mambobin Kawancen da su taimaka wa Turkiyya ta kowacce fuska.Labarai masu alaka