Erdoğan: Isra'ila na aikata ta'addanci da take hakkokin dan adam a Zirin Gaza

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya sake sukar ta'addancin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza inda ya ce, Kasar ta Yahudu na take hakkokin dan adam.

Erdoğan: Isra'ila na aikata ta'addanci da take hakkokin dan adam a Zirin Gaza

Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya sake sukar ta'addancin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza inda ya ce, Kasar ta Yahudu na take hakkokin dan adam.

A yayin abincin bude bakin azumin farko da aka shirya a fadar Shugaban Kasa da ke Beştepe inda ya ce, a yanzu ana aikata laifuka yaki da tae hakkokin dan adam a Kasar Falasdinawa da mutane Ma'asumai suka dauki tsawon shekaru suna kare wa. Ya ce, a ranar Litinin a lokacin da Amurka ke yunkurin bude ofishin jakadancinta a Kudus Falasdinawa 63 sun yi Shahada inda wasu dubu 3 suka samu raunuka.

Sakamakon hare-haren ta'addanci, rashin adalci da saba doka da Isra'ila ke kai wa ya sanya a cikin rabin karni an kasa samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kasar Falasdinawa.

Shugaban na Turkiyya ya ci gaba da cewa, mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Kudus da aka yi ya saba wa dokokin kasa da kasa da na Majalisar Dinkin Duniya. Sojojin Isra'ila na kashe wa tare da jikkata mutanen da ba sa dauke da makamai, ba sa rigima ko zalunci.

Ya ce, Zaluncin Isra'ila bai bar Falasdinawa yara kanana, tsofaffi da nakasassu ba.

Erdoğan ya jaddadawa duniya matsayin Turkiyya na kasance wa tare da Falasdinawa kuma za su ci gaba da adawa da zaluncin da Isra'İla ke yi.

 Labarai masu alaka