Turkiyya na ci gaba da gayyatar Musulmai hada karfi da karfe

Turkiyya na ci gaba da gayyatar shugabannin kasashen Musulmai zama tsintsiya madaurinki kan batun Qudus da Falasdinu.

Turkiyya na ci gaba da gayyatar Musulmai hada karfi da karfe

Turkiyya na ci gaba da gayyatar shugabannin kasashen Musulmai zama tsintsiya madaurinki kan batun Qudus da Falasdinu.

Firaministan Turkiyya Binali Yıldırım ya aika wa firaministar Bangaladesh,Sheikha Hasina,takwaransa na Morocco Sadeddin al-Osmani,na Pakistan Shahid Hakan Abbasi,na Qatar Sheikh Abdullah bin Nasır bin Halife Al Sani da na Aljeriya Ahmed Uyahya,goron gayyata don zuwa taron gaggauwa da kasashen Musulmai zasu yi a ranar Jumma'ar nan mai zuwa,da nufin tattauna matsalar Falasdinu da Qudus.

A cewar bayanan da aka samu daga ofishin firaministan Turkiyya,Yıldırım ya gana da Hasina, el-Osmani, Abbasi, Sheikh Abdullah da Uyahya ta wayar tarho.

A ganawar da yayi da firaministocin 5,shugaban gwamnatin Turkiyya yayi wa takwarorinsa barka da gabatowar watan Ramalana tare da gayyatar su zuwa taron gaggauwa da kasashen Musulmai za su shirya a birnin Santambul a karkashin jagorancin shugaba Erdoğan,don tattauna batun cuzgunawar da Isra'ila take yi wa Falasdinawa.

Shugabannin gwamnatocin kasashen 5,sun dauki alkawarin halartar taron tare da goya wa Turkiyya baya kan batun Falasdinu da Qudus da kuma taya Falasdinawa Alhini game da ukubar da suke ci gaba da fuskanta.Labarai masu alaka