Yahudawan Ingila: Isra'ila azzaluma ce,muna rokon Allah ya tarwatsa ta

Yayin wata ziyara da shugaban Turkiyya ya kai Ingila,tababban malamin Yahudu,Elahanan Beck da tawagarsa ta shiyyar Yahudawan Ortodox darikar "Neturei Karta" sun kai wa Erdoğan ziyara don jinjina masa kan batun Qudus.

Yahudawan Ingila: Isra'ila azzaluma ce,muna rokon Allah ya tarwatsa ta

Yayin wata ziyara da shugaban Turkiyya ya kai Ingila,tababban malamin Yahudu,Elahanan Beck da tawagarsa ta shiyyar Yahudawan Ortodox darikar "Neturei Karta" sun kai wa Erdoğan ziyara,don jinjina masa game namijin kokarin da yake ci gaba da yi na gasa aya a hannun shugabannin Isra'ila.

Bayan sun gana da shugaba Erdoğan malamin Yahudu Beck yayi jawabi gaban manema labarai a Landan,inda ya ce,

"Tallafa wa Yahudawan Sahyoniyawan Isra'ila mugun abu ne ga al'umar Yahudu.Idan kuna son taimaka wa Yahudawa to ku gaggauta goya wa Erdoğan baya".

Da yake magana kan shugabannin Amurka da kuma Ingila,Beck ya ce,

"Wanda duk ya tallafa wa Isra'ila,to ya san cewa ya cutar da Yahudawa".

Beck wanda ya ce ,ba wai tabo batun Falasdinawa kawai, a yau Isra'ila kasa ce mai babbar hatsari ga Yahudawa ma su kansu, haka zalika ya ce,

"Idan kuna son taimaka wa Yahudawa to ku gaggauta goya wa Erdoğan baya.Ku yi hanzari ku janye jakadojinku daga Isra'ila.Ku fita daga Isra'ila.Ku zama tsintsiya madaurinki daya don tunkarar ta.Muna Allah wadai da wutar tashin hankalin da ke ci gaba da ruruwa babu kakkautawa a yankin.Muna son mu dawo da zaman lafiya.A kulli Yaumin,muna rokon Allah ya tarwatsa Isra'ila.Bamu son kasashe 2.Fatanmu kasa daya tilo,watau Falasdinu.Muna son Falasdinawa suka dawowa gida.Yahudawa da Musulmai muna iya rayuwa tare kamar a baya, gabanin zuwan azzaluman Sahyoniyawa".

 Labarai masu alaka