Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Babban labarin jaridar Sabah na cewa shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya fara ziyarar ƙasar Azerbayjan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko. Shugaba Erdoğan da tawagarsa sun gana da shugaban kasar Azerbayjan İlham Aliyev inda suka gudanar da taron manema labarai akan inganta dangantakar kasashen biyu.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa bayan ziyarar farko da shugaba Recep Tayyip Erdoğan ya kai a Azerbayjan ya yada zango a Jamhuriyar Demokradiyyar Cyprus ta yankin Turkiyya inda ya suka gudanar da taron manema labarai da shugaban kasar Mustafa Akınci, shugaba Erdoğan ya bayyana cewar ba zasu bar Cyprus ita daya ba zasu cigaba da daukar matakan da suka dace domin warware matsalolin kasar.

Babban labarin jaridar Star na cewa Turkiyya ta bayyana farin cikin ta akan yadda kasashen Ethiopia da Eritrea suka warware matsalolin dake tsakanin su.

Babban labarin jaridar Star na cewa za'a gwada aikin jiragen yaƙin Turkiyya masu saukar ungulu 20 kirar ATAK a taron ƙolin kasashen NATO da zaa gudanar 11- 12 ga watan Yuli a Bruxelles babban birnin Beljiyom.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa yawan fasinjojin da kanfanin jiragen saman Turkiyya ke dauka ya karu da kaso 10.6 cikin ɗari a yayinda yake miliyan 6.3 a cikin shekara.Labarai masu alaka