Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.07.2018

Babban labarin jaridar Star na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya halarcin Babban Taron NATO a Brussels ya zama abun kokawar a tattauna da shi. A sanarwar bayan taro da aka fitar an bayar da muh,immanci wajen yaki da ta'addanci tare da Turkiyya.

Babban labarin jaridar Yeni Safak na cewa, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu da ya halarci taron NATO a Brussels ya aike da sako na musamman ga Kasashen Yamma. Cavusoglu ya kuma tabo masu sukar Turkiyya gameda sayen S-400 daga hannun Rasha da cewa Turkiyya na nesanta kanta daga NATO inda ya ce, da a ce NATO ta amince ta sayarwa da Turkiyya wadannan makamai da ta saya daga hannunsu. Nan da karshen shekara mai zuwa za su karbi batiran makaman daga hannun Rasha. Babu bukatar tuhumar wannan abu. 

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, an yanke hukuncin daurin rai da rai ga mamban NSU na karshe da ya rage Beate Zvape wanda ya kashe Turkawa 8, Bagirke 1 da dan sandan Jamus 1 a tsakanin shekarun 2000-2007. Turkiyya ta ce, wadanda suka yi amfani da sunan NSU na asali ba su bayyana a gaban kotu ba. Ba a bayyana alakar kungiyar da Daular Karkashin Kasa da ke Jamus ba.

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, a lokacin da samar da man zaitun ya ja baya a shekarun 2016/2017 a duniya, amma Turkiyya ta zama kasar da ta fi kowacce habaka nata. Turkiyya ta karra yawan man zaitun da ta ke samarwa da tan dubu 58 zuwa tan dubu 208.A yanzu Turkiyya ta zama ta 2 a duniya wajen samar da man zaitun. 

 Labarai masu alaka