'Wanda ya rike Allah, shi ne mai karfi..Ba mai iko ko kuma kudi ba'

Shugaban kasar Turkiyya,Recep Tayyip Erdoğan ya ce,ba zasu taba durkusa wa kasashen Yamma,wadanda suka gina rayuwa da kuma tarihinsu kan zalunci.

erdoğan.jpg

Shugaban kasar Turkiyya,Recep Tayyip Erdoğan ya ce,ba zasu taba durkusa wa kasashen Yamma,wadanda suka gina rayuwa da kuma tarihinsu kan zalunci.

Erdoğan ya furta wannan kalamin a ranar Asabar din nan, a albarkacin babban taron siyasa na jam'iyyar AKP na 6 wanda aka gudanar a Ankara,babban birnin kasar Turkiyya.

Shugaban na Turkiyya ya ce,

"Wasu na yi mana barazanar durkusar da tattalin arzikinmu, kakaba mana takunkumai,ninka kudin ruwa da kuma karya darajar kudinmu.To su sani cewa,an yi walkiya,komai ya fito karara.Mun gano manakisarku,ga fili mai doki.Mu je zuwa".

Erdoğan ya kara da cewa,

"Shin wanda ya yi imani da Allah, shakkun me zai yi ? Har abada,ba zamu taba durkusa wa kasashen Yamma,wadanda suka gina rayuwa da kuma tarihinsu,kan zalunci.Da Imani ne Turkawa suka warware dukannin ha'ince-ha'ince da kuma kulle-kullen da aka yi musu a baya.Ba zamu taba hada gwiwa da kasashen da ke nuna mana cewa su abokan ittifakinmu ne,alhali suna shirya mana gadar zare cikin duhu.Wanda ya rike Allah, shi ne mai karfi..Ba mai iko ko kuma kudi ba.Babu wata kasar da ta isa ta durkusar da al'umata,wacce ke shirye wajen sadaukar da rayuwarta don cimma manufofin da ta sa gaba.Muna kara jaddada muku cewa, ba zaku taba iya raba kanun al'umarmu,rugurguje kasarmu,sauke tutarmu,toshe muryoyin ladananmu,hana mu cigaba ko kuma cim ma manufarmu".

 Labarai masu alaka