Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.10.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.10.2018

Manyan labaran wasu jaridun Turkiyya 11.10.2018

Babban labarin jaridar Saban na cewa, Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yikira da su fara mu'amalar kasuwanci da kudaden kasashen tsakaninsu da kasashen Afirka. Erdogan ya yi jawabi a wajen bude taron kasuwanci na Turkiyya-Afirka a Istanbul inda ya ce " A lokacinda muke karfafa dukkan aiyukan jakadancinmu a nahiyar, Afirka ma ta kara yawan ofisoshin jakadancinta da ke Turkiyya daga 10 zuwa 33. Kawayenmu na Afirka suna bayar da goyon baya a aiyukan da muke na hada kai da yaki da rashin adalci a kungiyoyi da dama da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da Kuniyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC). A saboda haka ina kira ga 'yan Afirka da su fito su zo mu yi kasuwanci da kudadenmu" 

Babban labarin jaridar Hurriyet na cewa, Kamfanin Jiragen Saman Turkiyya Turkish Airlines zai fara sayar da tikitin tashin jirage ga sabon filin tashi dasaukar jiragen sama na Istanbul. Bayan an kaddamar da Babban Filin Turkishi Airlines zai sayar da tikitan safarar cikin gida da waje. A cikin gida za a fara sayar da tikitin zuwa Izmir, Adana, Ankara, Antalya, Baku da Jamhuriyar Turkiyya da ke Arewacin Cyprus. Turkish Ailins ne zai yi jigilar kaso 70 na fasinjoji a sabon filin tashin jirgin. A tsakanin 30-31 ga Disamba ne za a kammala koma wa sabon filin jirgin na Istanbul gaba daya.

Babban labarin jaridar Vatan na cewa, a daidai lokacin da dakarun Turkiyya suke ci gaba da karbar jiragen yaki masu saukar ungulu na ATAK, ana ci gaba da samar musu da sabbin jiragen. Za a kara kara yawan hanoyin sadarwa sannan za a samar da sabbin manhajoji. An fara iyukan samar da injinan jirgin a cikin gida.Labarai masu alaka