Jami'an tsaro sun fafata da ƴan ta'adda a Turkiyya

Jami'an tsaro a garin Varto dake yankin Mus dake kasar Turkiyya sun fafata da yan ta'addar PKK a inda suka yi nasarar kashe daga cikin ƴan ta'addar biyar.

Ofishin magajin garin yankin ta bayyana cewar jami'an tsaron yankin Varto sun kewaye kauyen Yilanli bayan sun samu labarin ƴan ta'addar sun maida ƙauyen gurin shaƙatawa. 

Akan hanyar kauyen ma jamian tsaro sun kwashi artabu da wasu yan ta'addar dake cikin wata mota bayan sun ƙi tsayawa bincike.

A yayin artabun an kashe daga cikin yan ta'addar mata biyu da maza uku.

Ana dai ci gaba da fatattakar ƴan ta'addar yankin domin kuɓutar da al'ummar yankin daga uƙubar ta'addanci.

 Labarai masu alaka