Turkiyya ta share kwallan marasa gatan Sham

Babbar Hukumar bada gaji ta Turkiyya, ta aika tireloli 316 cike makil da kayayyakin masarufi da kuma tufafi zuwa Siriya da zummar share hawayen marasa galihun wannan kasar,wacce rikice-rikicen suka durkusar.

Turkiyya ta share kwallan marasa gatan Sham

Babbar Hukumar bada gaji ta Turkiyya, ta aika tireloli 316 cike makil da kayayyakin masarufi da kuma tufafi zuwa Siriya da zummar share hawayen marasa galihun wannan kasar,wacce rikice-rikice suka durkusar.

Hukumar ta fitar da wata rubutacciyar sanarwa game da tallafin da ta ke ci gaba da bai wa al'umomin da ke a yankunan daban-daban na Siriya,inda Turkiyya ta kaddamar da farmakan tsaro na Firat da na Reshen Zaitun.

A sanarwar,an tabbatar da cewa,a wadannan yankunan, shugabannin Turkiyya sun gina ofisoshin bada tallafi biyar,wadanda su ne ke da alhakin raba wa mabukata kayayyakin taimako.

A bara hukumar ta ciyar da akalla iyalai dubu 15,000 da ke rayuwa a sansanonin masu neman mafaka na garin Azez da ke yankin Aleppon kasar Siriya.

Haka zalika,ta sabunta masallatai 160 wadanda aka rusa yayin tashe-tashen hankula da kuma sake gina wasu 268,wadanda dukannin su an fara gudanar da ibade a cikin su a karshen shekarar bara. 

Tun a lokacin da yaki ya barke a Siriya ya zuwa yau,Turkiyya ta aika akalla tireloli 866 don tallafa wa fararen hular kasar wadanda ke cikin halin ha'ula'i.Labarai masu alaka