Daruruwan sojojin Somaliya na ci gaba da samun horo na musamman daga takwarorinsu na Turkiyya

Somaliyawa na cigaba da aika sakon godiyarsu zuwa ga shugaba Recep Tayyip Erdoğan, wanda a karkashin inuwarsa ne,Turkiyya ke ci gaba da horar da dararuwan sojojin kasarsu da zummar dakile annobar rashin tsaro da ya jefa su halin ha'u-la'i, da kuma yin ka-in-da-na-in a wajen samar musu da ingantaccen ilimi da cikakken koshin lafiya.