UEFA: Beşiktaş ta doke Leipzig da ci 2 da 1

Kungiyar Kwallon Kafar Turkiyya ta Beşiktaş ta doke takwararta ta kasar Jamus da ci 2 da 1 a wasan mako na 6 kuma na karshe a rukunin G na gasar Zakarun Turai ta UEFA.

A minti na 10 dan wasan Beşiktaş Negredo ya ci kwallo da bugun daga kai sai mai tsaron gida sai a minti na 90 Taslica ya kara jefa kwallo ta 2 a ragar Leipzig.

Dan wasan Leipzig Keita kuma ya samu damar jefa kwallo 1 a ragar beşiktaş.

Beşiktaş ta kammala wasan rukunin da maki 14 inda ta samu nasarar kara sama a jadawalin gasar.Labarai masu alaka