Kane ya zama dan wasan da ya fi kowanne jefa kwallaye a kakar wasanni ta bana a Turai
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane ya zama zakaran dan wasan bana da ya fi kowanne jefa kwallo a kakar wasanni ta bana a nahiyar Turai inda ya jefa kwallaye 56 a raga.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Harry Kane ya zama zakaran dan wasan bana da ya fi kowanne jefa kwallo a kakar wasanni ta bana a nahiyar Turai inda ya jefa kwallaye 56 a raga.
A wasan da Tottenham ta buga da Southampton dan wasa Kane ya jefa kwallaye 3. A yanzu kungiyar na kan mataki na 4 da maki 37 a jadawalin gasar.
Kane ya haura Alan Shearer da a shekarar 1995 ya jefa kwallaye 36 a raga a kakar wasanni daya.
Kane dan kasar Ingila ya ciri tuta bayan jefa kwallaye 56 a gana.