'Yan wasan kwallon kafa sun fi sha'awar zuwa Turkiyya don taka leda

'Yan wasan kwallon kafa a duniya sun nuna sun fi son zuwa Turkiyya don taka leda sakamakon yadda ake biyan haraji mara yawa a kasar.

'Yan wasan kwallon kafa sun fi sha'awar zuwa Turkiyya don taka leda

'Yan wasan kwallon kafa a duniya sun nuna sun fi son zuwa Turkiyya don taka leda sakamakon yadda ake biyan haraji mara yawa a kasar.

A watan Disamba ne majalisar dokokin Turkiyya ta ce, har nan da karshen shekarar 2019 'yan wasan kwallon kafa da ke Turkiyya za su ci gaba da bayar da harajin kaso 15 cikin 100 a matsayin haraji ga kasar.

Farfesa Sebahattin Devecioglu na sashen wasanni da ke jami'ar Firat ya ce, manufar saukaka harajin ita ce karfafa gwiwa ga yadda masu horar da 'yan wasa da 'yan wasan suke nuna sha'awar zuwa Turkiyya.

Akwai 'yan wasan kasashen waje da dama da ke taka leda a kungiyoyin kwallon kafa na Turkiyya.Labarai masu alaka