Ronaldo zai fara shirya fina-finai

Shahararren dan wasan kwallon kafa,Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa,yana gaf da zama mashiryin fim.

Ronaldo zai fara shirya fina-finai

Shahararren dan wasan kwallon kafa,Cristiano Ronaldo ya wallafa a shafinsa na sada zumunta  cewa,yana gaf da zama mashiryin fim.

A wannan karon,dan wasan wanda tuni tauraruwarsa ta haska a fannoni kamar su kwallon kafa,siyar da tufafi da kuma kasuwanci,zai rungumi sana'ar shirya fina-finai masu babuka wato Series a Turance

A cewar wani labari da aka wallafa a jaridar babbar masan'antar shirya fina-finai ta Hollywood ta Amurka,a fim din da Ronaldo zai shirya,za a nuna rayuwar wasu 'ya 'ya mata masu kwallon kafa wadanda suka fito da kasashe daban-daban.

Fitattun masu bada umarni a duniyar fina-finai, Liz Garci da Josh Harto ne za su yi ruwa da tsaki wajen tsara wannan shirin na Ronaldo.

Da yayi bayani a shafinsa na sada zumunta,Ronaldo ya ce,

"Kallon talabiji na daya daga cikin ababen da na fi sha'wa.Wannan fim da zan shirya tare da tallafin kwararru a fagen fina-finai na duniya,wata babbar dama ce a gare ni wajen shiga duniyar fina-finai wacce ni bakonta ne".

 Labarai masu alaka